Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa manyan motocin
daukar kaya fiye da 300 daga Burkina Faso sun isa birnin Niamey a kokarin da kasar ke yi na ragewa yan Nijar radadin takunkuman da aka Sanya musu.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasashen Benin da
Najeriya manyan kasashen da ake shigar da abinci jamhuriyar Nijar suka rufe
iyakar su da kasar wadda ke karkashin juyin Mulki.
Tun bayan juyin mulkin na
Nijar ta ke samun goyon bayan gwamnatin kasashen Burkina Faso da Mali, abinda masana
ke ganin hakan yana da alaka da kasasancewar su sojoji.
Bayanai sun ce motocin makare
da kayan abincin sun sami rakiyar sojojin Burkina Faso, kafin daga bisani suka
mikasu hannun sojojin Nijar akan iyakar kasashen biyu.
Ko da yake jawabi daraktan
hukumar hana fasa kwauri ta jamhuriyar Nijar Kanal Adamou Zaraoumeye yace hukumar
sa ta karbi motoci guda 300 makare da kayan abinci da suka hadar da masara da
gishiri da sauran kayan masarufi.
A cewar sa nan ba da jimawa
ba za’a far araba ayan ga jama’ar kasar da nufin rage musu radadi.