An garzaya da kocin Man City Guardiola Asibiti


Mai horar da 'yan wasan kungiyar Manchester City Pep Guardiola ba zai samu jagorancin kungiyar ba har na wasanni biyu da za ta buga nan gaba sakamakon wata tiyatar gaggawa da za a yi masa a gadon bayansa.


Guardiola wanda yanzu haka yana Barcelona inda aka yi masa tiyata yana kuma murmurewa ana sa ran ba zai jagoranci City ba a wasannin da za ta yi da Sheffield United a wannan Lahadi da Fulham a ranar 2 ga Satumba ba, inda mataimakinsa Juanma Lillo zai maye gurbinsa na wucin gadi.

City ta ce kocinta wanda ya jagoranci yan wasanta suka lashe kofina uku rigis a kakar da ta gabata na fama da "matsanancin ciwon baya na " kuma tuni aka fita da shi zuwa birnin Barcelona don domin yi masa tiyata.

Post a Comment

Previous Post Next Post