AU ta kori jamhuriyar Nijar daga cikin ta

Kungiyar tarayyar Africa ta sanar da korar jamhuriyar Nijar daga cikin ta, abinda ke zama wani hukunci na baya-bayan nan da aka yankewa Nijar bayan juyin Mulkin watan jiya.

Bayan taron kungiyar na yau Talata a birnin Addis Ababa, kungiyar ta ce daukar wannan mataki ya zama wajibi la’akari da yadda sojojin na Nijar suka ki bada hadin kan da ya dace a game da tattaunawar Diplomasiyya.

Matakin na AU na zuwa ne bayan da tuni ECOWAS da wasu kungiyoyin kasashen ketare suka sanar da kakabawa Nijar din takunkumai, wadanda tuni suka fara tasiri a kanta.

Sai dai kuma masana na ganin cire Nijar daga cikin AU ba zai yi mata wani tasiri ba, la’akari da yadda kungiyar ke zama tamkar dai ‘yar amshin shatan kasashen yamma a wasu lokutan.

Bayan wannan mataki, kungiyar ta AU ta kuma ce zata bibiyi irin matakan da kungiyar ECOWAS ko CDEAO ta dauka kan jamhuriyar Nijar, don ganin ta inda ya kamata ta kara shiga da nufin kara matsa lamba ga sojojin na Nijar.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp