Gwamnatin Najeriya
ta kwaso yan asalin kasar 161 da aka daure su a gidajen yarin kasar Libya daban-daban
sakamakon aikata laifukan da suka sabawa ka’idar yin kaura.
Jakadan Najeriya a Libya Ambasada Kabiru Musa ne ya bayyana hakan a wata
sanarwa da ya fitar ga manema labarai a birnin tarayyar kasar Abuja.
A cewar Ambasada Musa gwamnatin Najeriya
ta rika kai gwauro da kai mari wajen ganin an saki mutanen da aka garkame a
gidan yarin don basu damar komawa gida, da nufin sake gina rayuwar su.
Sanarwar ta kuma kara da cewa tuni
mutanen suka isa Najeriyar, yayin da aka gargade su da su kaucewa yunkurin tsallakawa
zuwa turai ta barauniyar hanya don gudun fadawa hannun hukumomi ko kuma bata
gari.
Wannan dai ba shine karon farko da ake samun 'yan Najeriya da dama na
tsallakawa zuwa turai da saharar Libya ba, inda kuma a mafi yawan lokuta suke
gamuwa da masu garkuwa da mutane ko yan fashi ko kuma a wasu lokutan su ci karo da jami’an tsaro.