Ba zan iya sayar da “manpower” ko kayan mata a Saudiyya ba - Sadiyya Haruna

Sadiyya Haruna ta ce ba za ta iya sayar da kayan da take sayarwa a Nijeriya a kasar Saudiyya ba. 

A cikin gajeran bidiyo da ta wallafa, ta ce, ta gode da arzikin da Allah ya yi mata a Nijeriya; ba ta bukatar daukar maganin maza da kayan mata zuwa kasa mai tsarki. 

Fitacciya a shafukan sada zumunta da aka jima ana zargin ta da batsa ta hanyar sayar da wadannan kayayyaki na shan cece-kuce a baya-bayan nan a kan tangardar da aurenta da mawaki G-Fresh ke fuskanta.

A wata hira da Sadiyya Haruna ta yi da DCL Hausa a 2021, ta ce, ba ta jin kunyar wadannan kayayyaki da take sayarwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post