Ministocin Tinubu za su lakume Naira bilyan 8.6 matsayin albashi


Gwamnatin Shugaba Tinubu za ta kashe kudi Naira bilyan 8.6 wajen biyan albashi da alawus-alawus cikin shekaru 4 na ministoci 48 da aka nada.

Daily Trust ta rawaito cewa jimillar kudin ta kai haka ne bayan da hukumar tattarawa da rarraba kudaden shiga ta kammala bitar albashi da alawus-alawus na manyan ma'aikatan gwamnati.

Sai dai wani kwararru a bangaren tattalin arziki ya sanar da manema labarai cewa yawan kudin ya ci karo da kudiri ko jawabin Shugaba Tinubu na farko, da ke cewa zai rage yawan kudaden da ake kashewa jami'an gwamnati.

Kwararrun suka ce nada wadannan ministocin da yawa, shi zai sa su ma su nada masu taimaka musu na musamman da hakan zai kara nauyi ta gwamnati.

Lokacin farko dai kenan da aka samu yawan ministoci a Nijeriya sun kai 48 tun 1999 da aka dawo dimokradiyya. Zamanin tsohon shugaban kasa Buhari na da ministoci 42.

Tsohon shugaban kasa Good luck Jonathan na da ministoci 33 sai Marigayi Umaru Musa Yar'adua ya yi ministoci 39. Shi kuwa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi ministoci 42.

Post a Comment

Previous Post Next Post