Sojojin mulkin Nijar sun sauke shugabannin jami'o'in Agadez da Zinder


Hukumomin mulkin sojan Nijar sun cire shuwagabannin jami'o'i biyu daga mukamin su

A cikin wata sanarwa ce da suka fitar hukumomin mulkin sojan Nijar suka bayyana cire wasu malaman jami'a daga mukamman da suke rike da su a cikin jami'o'in daban daban ciki kuwa har da shuwagabannin jami'o'in Agadez da Zinder 

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wani gungunsu na malaman jami'ar da ya kunshi malaman 37 ya fitar da wata sanarwa wacce a ciki suka nisanta kansu da wata sanarwar ta daban da kungiyar ta SNECS ta fitar wacce a ciki ta kawo goyan bayan ta da sunan dukkan malaman ga sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar

Shi dai wannan gungu na malaman jami'ar ya ce ko alama ba ya goyan bayan wannan juyin mulki

Kazalika wata sanarwar ta daban da kakakin gwamnatin rikon kwaryar ta Nijar ya karanta na cewa an kawo karshen aikin sakataren ma'aikatar ilimi mai zurfi tare da shugaban hukumar da ke kula da jarabawar Baccalauréat da ake kira da OBEECS

Wasu rahotannin kuma na cewa tuna aka kira daya daga cikin malaman Pr Malaman Issa an kiraye shi ofishin jami'an tsaron na Gendarmerie

Post a Comment

Previous Post Next Post