Tinubu nake yi wa aiki ba APC ba kuma har yanzu ina PDP - Nyesom Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya ce shi fa shugaba Tinubu yake yi wa aiki ba wai jam'iyyar APC ba.

Tsohon Gwamnan na jihar Rivers ya ce yana yi wa shugaban kasar aiki ne don ya aminta da shi har ya damka masa amana. Wike ya fadi haka ne a lokacin da ya halarci shirin siyasa na gidan talabijin na Channels.

Ya ce ban yi nadamar cewa ina PDP na yi wa shugaba aikin da ya ci zabe ba.

'Yan Nijeriya na ta tofa albarkacin bakinsu game da yiwuwar kasancewar Wike a jam'iyyar PDP ganin yadda aka nada shi minista kuma sunansa ya fito a jerin mambobin kwamitin yakin neman zaben Gwamna a jihohin Imo, Bayelsa da Kogi a zaben da zai gudana a Nuwambar 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post