Kwamitin wucin-gadi na majalisar wakilan Nijeriya da ke bincike kan yadda aka alkinta kudaden kula da muhalli ya sa kafa ya shure batun da hukumar kula da muhalli ta kasa ta yi na cewa ta kashe Naira bilyan 81 wajen sayowa tare da dasa itatuwa milyan 21 a jihohin da ke fama da matsalar zaizayar kasa a arewacin Nijeriya.
Jihohin su ne na Kebbi, Katsina, Sokoto Zamfara, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Adamawa, Yobe da Borno.
Darakta Janar na hukumar Yusuf Maina Bukar ya fada wa 'yan kwamitin cewa hukumar ta kuma kashe kudi Naira milyan 697.71 wajen gyaran ofisoshi da Naira bilyan 11.28 wajen gudanar da manyan ayyuka.
Shugaban kwamitin Isma'ila Haruna Dabo, ya sanar da cewa hukumar ta kashe kudi kawai ba tare da an ga alfanun hakan ba. Kazalika, kwamitin ya ce wannan hukuma ta kauce daga irin tsarin aikin da aka kafa ta.