Duk sojan da ba zai yi wa Tinubu biyayya ba, ya ajiye aikin - Janar TakutiBabban Kwamandan rundunar soji ta 81 Manjo Janar Muhammad Takuti Usman ya bukaci jami'an soji a Nijeriya da su ci gaba da yi wa shugaba Bola Tinubu da duk wanda kundin tsarin mulkin kasa ya umurce su biyayya.

Janar Takuti Usman na magana ne a lokacin da ya ziyarci rumbun adana makamai na 35 Artillery Brigade da ke Alamala, Abeokuta jihar Ogun.

Kwamandan sojin ya bukaci sauran sojojin da su kasance masu biyayya tun daga sama har kasa. Kalaman nasa dai na zuwa ne a lokacin juyin mulki ke ta kara fadada a Nahiyar Afrika, a yayin da aka hambarar da gwamnatin Ali Bango na kasar Gabon.

Janar Takuti ya ce rundunar sojin Nijeriya ba za ta lamunci duk wani nau'in rashin da'a ba daga jami'anta ko ma wani daga waje, inda ya ce akwai 'yan matsaloli nan da can, amma dai ba a wannan sashen adana makamai ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post