Gwamnatin Kano ta sayo gadajen Aurar da zawarawa 1,800

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta sayo kayan daki na ma'aurata 1,800 a karkashin shirinta na aurar da zawarawa a fadin jihar.

Babban kwamandan hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da wasu daga cikin kayayyakin auren a ranar Laraba a Kano.

Ya ce gwamnati jihar ta ware kudi sama da Naira miliyan 800 don siyan kayan daki da kayan abinci da kayan sawa da sauran kayan bukatu na bikin auren na zawarawa da za ta kaddamar.

Post a Comment

Previous Post Next Post