Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya jaddada
muhimmancin ilimin tarihi wajen gina kasa. Maitamaki na musamman kan harkokin yada labarai ga Atikun ya ce Waizrin Adamawa ya ambata hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin ayarin
hukumar editocin jaridar The Sun karkashin babban editan ta Mr. Onuoha Ukeh
yayin da suka kai masa ziyara a gidan sa da ke Abuja a wannan Talata.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Wanda yanzu haka ke
kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa a gaban kotu, kasancewar sa wanda ya
yiwa jam'iyyar PDP takara, ya ce ba tare da la'akari da darrusan da tarihi ya
nuna ba, za a ci gaba da maimaita kura-kuran da aka tafka a baya. Yace wadanda
suke zaune ba tare da sanin abin da ya gabace su ba, akwai yuwuwar su aikata
kura-kuran magabata, inda ya ce ba daidai ba ne a cire darasin tarihi daga
manhajar koyarwar makarantun Nijeriya.