Ruftawar gini ta yi ajalin mutane a sansanin 'yan gudun hijira na Borno

 


Rahotanni daga birnin Maiduguri na cewa mutane 7 sun mutu a sakamakon faduwar gini a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke birnin Maiduguri na jihar Borno.

Jami’an kungiyar Civilian JTF sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa wani aji ne ya fado kan wasu mutane da ke kwana a ciki sanadin ruwan sama a garin Munguno.

Bayanai sun ce ginin ya fado ne da misalin karfe 7 da rabi na safiyar yau, kuma nan take mutane 7 suka ce ga garin ku nan.

Wasu jami’an lafiya sun tabbatarwa manema labarai cewa akwai mutane fiye da 20 yanzu haka da ke kwana a babban asibitin garin Munguno suna karbar magani bayan raunukan da suka gamu da su.

Garin Munguno da ke da nisan kilomita 85 zuwa birnin Maiduguri na da ‘yan gudu hijira fiye da dubu 40 wadanda suka gujewa ta’addancin Boko Haram daga garuruwan su.

Post a Comment

Previous Post Next Post