Jam’iyyar NNPP Ta dakatar da jagoran jam’iyyar Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, kan zargin sa da yiwa jam’iyyar zagon kasa.
Haka kuma jam’iyyar ta dakatar da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar baki daya.
Baya ga wannan dakatarwa kwamitin zartawar ya nada Dr. Abgo Major a matsayin mai rikon mukamin shugaban kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da kuma Mr. Ogini Olaposi a matsayin mai rikon mukamin sakataren jam’iyyar da wasu Karin mukamai 18.
Kamafanin dillancin labarai NAN ya ruwaito cewa dakatarwar ta tsahon wata shida ce ko kuma idan aka lura jagora kwankwason ya daidaita sahun sa kan zarge-zargen da ake yi masa.
Ko a ranar 24 ga watan da muke ciki na Agusta sai da Kwamitin ayyuka na hukumar ya dakatar da wanda ya kirkiri jam’iyyar Dr. Boniface Aniebonam da kuma jami’in yada labaran jam’iyyar na kasa.
A baya dai jam’iyyar ta yi barzanar sallamar kwankwaso matukar bai daina bibiyar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da bibiyar ‘yan jam’iyyar APC ba, duk a kokarin da yake yi na ganin an bashi mukami kamar yadda ta yi zargi, sannan ta shawarce shi kan ya koma jam’iyyar da yake kwadayi salin alin, matukar zai zama cikakken dan jam’iyyar NNPP .
Category
Labarai