Babbar kotun jihar Kano ta haramtawa EFCC da wasu hukumomi bincikar Muhuyi

Babbar Kotun jihar Kano ta haramtawa Hukumar EFCC da kuma ta da’ar ma’aikata wato CCB daga kamawa ko kuma bincikar shugaban hukumar yaki da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano Muhuyi Magaji Rimin gado.

A wata takarar dakatar da bincike da kotun ta bayar karkashin jagorancin mai shari’a Farouk Lawan ta ce hukumomin biyu basu bi hanyar da ta dace wajen dakatar da shugaban hukumar daga aikin sa na binciken hukumomi ko dai-daikun mutane ba.

Tun farko dai Antoni Janar na jihar Kano Lwan Musa Abdullahi shine ya shigar da karar yana mai bukatar kotu ta dakatar da EFCC da sauran hukumomi masu biye mata baya wajen bincika ko kuma kama Muhuyi koma dakatar da shi daga wani aiki da yake yi.

Ta cikin takarar da korafin da Antoni Janar din ya aikewa kotun ya yi karin hasken cewa bisa doka matukar wadannan hukumomi na bukatar bincike ko kuma tuhumar wani ma’aikaci ko shugaban wata hukuma a Kano ya zama wajibi su tuntubi Ofishin sa.

Takardar ta kuma kunshi jawabin cewa hukumomin basu yi biyayya ga waccan doka ba, suka yi gaban kansu wajen aikea da Muhuyi takarda, don haka basu da hurumin kama shi ko tuhumar sa, har sai Antoni na jihar Kano ya Amince.

Sai dai alkali Faruk Lawan ya sanya wata rana da yake bukatar jin hanzarin dukannin bangarorin biyu a lokaci guda.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp