Jiga-jigan NNPP na neman Kwankwaso ya sauka daga jagorancin jam'iyyar saboda zargin zagon-kasa

Kungiyar shugabannin jam'iyyar NNPP na jihohi a Nijeriya sun yi kira ga jagoranta na kasa Engr Rabi'u Musa Kwankwaso da ya gaggauta yin murabus daga jam'iyyar ko su fatattake shi da karfin tsiya.

Jiga-jigan jam'iyyar sun ce su na zargin Kwankwaso wanda shi ne ya yi wa jam'iyyar takarar shugabancin Nijeriya a zaben 2023, na yi wa jam'iyyar zagon-kasa.

Sannan sun ce su na bukatar Rabi'u Kwankwaso da ya yi musu bayani dalla-dalla kan irin alakar da suka ga na wanzuwa tsakaninsa da jam'iyyar APC.

A cikin wata sanarwa daga Shugaban jiga-jigan jam'iyyar ta NNPP Sunday Oginni, ta zargi Kwankwaso ta hura wutar rikici a jam'iyyar domin ya yi uwa makarbiya da jam'iyyar daga wadanda suka kafa ta.

Post a Comment

Previous Post Next Post