Cutar mashako ta diphtheria ta hallaka mutane 122 a Nijeriya - UNICEF


Ofishin Najeriya na Asusun Tallafa wa Ilimi da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) na yayata irin ƙoƙarin da ya ke yi na ganin an shawo kan yaɗuwar annobar cutar mashaƙon da ke shafar ƙananan yara a jihohi guda 27 a kasar. Izuwa watan Yuli na shekakar 2023, an sanar da waɗanda ake zargin sun kamu mutum 3,850, waɗanda aka tabbatar da kamuwar mutane 1,387 da cutar ta mashaƙo. Abin tashin hankali shi ne, an rasa rayuka mutane 122, wanda yawan mace-macen ya kai kaso takwas da ɗigo bakwai cikin ɗari 8.7%.

Ɓarkewar cutar ta fi shafar Jihohin Kano da Yobe da Katsina da Ikko da Abuja da Sakkwato da kuma Zamfara, waɗanda suka bayar da kaso casa’in da takwas cikin ɗari na waɗanda suka kamu da cutar.

Yawancin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar, waɗanda a taƙaice sun kai kaso saba’in da ɗaya da rabi cikin ɗari sun shafi ƙananan yara ne waɗanda suke daga shekaru 2 – 14. 

Kamar yadda wakilin Ofishin Nijeriya na Asusun Tallafa wa Ilimi da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), Ms.Cristian Munduate ta faɗa, "Abu ne mai matuƙar sosa rai jin cewa kaso ishirin da biyu cikin ɗari 22 %  ne kawai aka yi wa allurorin rigakafi da ake yi wa ƙananan yara.

"Yawancin waɗannan ƙananan yara da suka kamu da cutar mashaƙon, musamman waɗanda suka rasu, suna cikin waɗanda ba a yi wa allurorin rigakafin ko sau ɗaya ba. Buƙatar da ake da ita ta sanar da waɗanda ba a iya kaiwa gare su ba wani abu ne mai wuya ba."

Domin ganin an ɗauki mataki kan ɓarkewar cutar,  Asusun Tallafawa Ilimi da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) na haɗin gwiwa da Cibiyar Shawo kan Yaɗuwar Cututtuka (NCDC) da Jihohin da abin ya shafa da Hukumar Kulawa da Bunƙasa Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA) don ganin an bayar da taimako da tallafawa don ganin an yi tsari da kuma tabbatuwar ɗaukin da za a kai. Jajircewa da taimakon Asusun Tallafawa Ilimi da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya faɗaɗa har zuwa nau’o’in tallafi daban-daban da suka haɗar da:

•Tsarawa da aiwatarwa da kuma tallafawa wajen sanar da bayanai game da afkuwar haɗura, sai kuma ayyukan da suka shafi sanya jama’a cikin ayyukan da suka shafi al’umma.

•Ɗaukar nauyin safarar kayayyakin rigakafi da sauran kayayyaki masu alaƙa da su izuwa jihohin da abin ya shafa, sai kuma ƙarfafa yin rigakafi akai-akai. 

•Bayar da horo ga jami’an Kula da lafiya da masu aikin sa-kai wajen ayyukan al’umma, sanar da afkuwar wasu haɗura da shigar da jama’a cikin ayyukan al’umma.

•Sanya ido kan ayyukan kai ɗauki game da ɓarkewar cututtuka.

•Nemowa da samar da takunkumin rufe fuska da sinadaran tsaftace hannu da magungunan samun kariya daga cutar mashaƙo. 

•Samar da kayayyakin amfani a ɗakin gwaje-gwaje da kayayyakin yi wa waɗanda ake zargin sun kamu gwaje-gwajen a Cibiyar Shawo kan Yaɗuwar Cututtuka (NCDC).

Ms Munduate ta ƙarfafa buƙatuwar da ake da ita na ganin an sami yaran da ba a iya yi wa rigakafin ba sakamakon hana shige da fice a yayin ɓarkewar cutar (COVID-19). Ya cigaba da cewa, “Yawancin yara ba a sami damar yi musu rigakafi ba a lokacin da aka hana shige da fice sakamakon ɓarkewar annobar KWABID (COVID-19). "Dole ne yanzu mu tashi tsaye don ganin mun cike wannan giɓin. Yaran da ba a yi musu rigakafin ko ɗaya ba, wato waɗanda ba a taɓa yi musu ba, su ne babbar damuwarmu."
Dangane da wannan ƙididdiga mai ban takaici,  Ofishin Nijeriya na Asusun Tallafawa Ilimi da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) na kira da iyaye da wakilan ‘ya’ya da su tabbatar sun kai yaransu an yi musu rigakafi don kare su daga cututtukan da ake iya yin rigakafinsu, kamar cutar mashaƙo. Asusun na UNICEF zai ƙara ƙaimi wajen ganin an shawo kan wannan cuta da ta ɓarke da kuma yin aiki tare da hukumomi don ganin tabbatuwar lafiyar al’umma da kuma ganin kyautatuwar rayuwar yara ‘yan Nijeriya ta nan gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post