Akwai bukatar a kara yawan hutun haihuwa ga mata ma'aikata daga watanni 3 zuwa 6 - UNICEF


Asusun kula da kanan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya ce akwai bukatar mahukunta su duba yiwuwar tsawaita wa'adin hutun haihuwa ga mata maaikatan gwamnati daga watanni 3 zuwa watanni 6.

Hakan kamar yadda babban jami'in UNICEF na Nijeriya Mr Rahama Rihood Mohammed Farah, ya sanar a bikin zagayowar makon shayar da nonon uwa na 2023 a Katsina, ya ce na da nufin ba iyaye mata damar shayar da jariransu sosai ba tare da an samu wata tangarda ba.

A sakon da Mohammed Farah ya aike da shi, da kwararre akan abinci mai gina jiki Mr Oluniyi Oyedokun ya karanta, ya kara kira ga mahukunta da su samar da wurare na musamman a ma'aikatun gwamnati da iyaye mata masu shayarwa za su rika shiga su na shayar da 'ya'yansu yadda ya dace da ware wasu sa'o'i a matsayin lokuttan fita a shayar da jarirai.

A taken bikin na bana, 2023 "Ba da dama ga masu shayarwa - samar da yanayi mai kyau ga iyaye mata masu shayarwa da ke aiki", UNICEF ta yi kira ga iyaye mata da ke shayarwa da su rika neman hakkinsu a ko'ina idan batun shayar da jariransu ya taso domin gudun kada 'ya'yansu su kamu da cutar tamowa.

Sannan UNICEF ta bukaci matan da ke da ilmin zamani, su rika bincike don shiga kwasa-kwasan da za su tallafe su wajen inganta lafiyar 'ya'yansu.

Taron na bana, da Asusun UNICEF ya shirya hadin guiwa da hukumar lafiya a mataki farko ta jihar Katsina suka shirya, an kuma yi kira ga masu rike da sarautun gargajiya, malaman addini, manema labarai da kungiyoyin fararen hula da su hada hannu wajen yekuwa kan shayar da jarirai nonon uwa zalla don tabbatar da lafiyar yaran da farincikin iyayensu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp