Mutanen Nijar na aza tambaya kan matsayar Seini Oumarou

Kakakin majalisar dokokin Nijar Alhaji Seini Oumarou ya nuna damuwa kan takunkuman da ECOWAS da UEMOA suka saka wa Nijar.

Alhaji Seini Oumarou ya nuna wannan damuwa ce a cikin wani sako da ya isar ga al'umma ta hanyar wata takarda da ke yawo a shafukan sada zumanta na zamani inda a ciki ya ce talakawan da ba su ji ba, ba su gani ba ne za su fi dandana kudar su a cikin wannan mataki na kungiyoyin biyu da suka dauka, don haka ya ce wannan mataki ba komai zai yi ba face kara dagula al'amuran kasar ciki har da na tsaro da 'yan kasar ke ciki daman.

Kazalika ya ce a ganinsa wannan mataki sam sam bai da ce da wanda zai kawo karshen matsalar da ake ciki ba yanzu, don haka ya ce yana kira da a hau teburin sulhu.

Sai dai wani abin mamaki a cikin wannan sako na shugaban jam'iyyar ta MNSD Nassara babbar jam'iyyar kawancen ta PNDS shi ne, rashin yin Allah wadai da wannan juyin mulki tare da kin yin kiran sakin shugaba Bazoum sai kuma kiran kansa a da tsohon shugaban majalisar dokokin a inda ya saka hannu a kasan takardar.

Post a Comment

Previous Post Next Post