JIBWIS ta tara Naira milyan 90 daga kudin fatun layya a bana


Kungiyar JIBWIS ta ce a bana ta tara kudin fatun layya da resitai da jimillar kudaden suka kai kimanin Naira miliyan casa'in, da dubu dari takwas da hamsin da biyar, da dari biyar da arba'in da biyu kacal  (90,855,542.00) a wannan shekara ta 2023.

Shugaban kungiyar IZALA a Nijeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya sanar da hakan bayan ya karbi rahoton kwamitin wanda shugaban kwamitin Sheikh Habibu Yahaya kaura ya ba da a garin Rano da ke jihar kano a ranar alhamis din nan.

Sheikh Bala Lau ya yaba wa 'ya'yan kungiyar da suka yi hobbasa wajen ganin sun mika fatun layyansu ga kungiyar ta IZALA, ya kuma sha alwashin ci gaba da ayyukan raya addini kamar yadda aka Saba da kudaden a baya, ta yadda ko da wanda ya ba da ya koma ga Allah, zai ci gaba da samun lada mai gudana daga Allah Insha Allah.

A bana jihar kaduna ce ta zo ta farko, inda ta samar da:
N11,127,650.00.

Jihar Sokoto ita ta zo na biyu inda ta tara:
N10,967,080.00

Sai jihar Kebbi ita tazo na uku inda ta tara:
N9,185,397.00

Jihar Katsina ita ce ta hudu inda ta tara:
N6,284,930.00

Jihar Niger ta zo ta biyar inda ta tara:
N5,529,665.00

Juhar Zamfara ita ke biye da su inda ta yi na shida ta tara 
N5,042,380.00

Jihar Adamawa ita tayi na bakwai inda ta tara:
N4,736,820.00

Jihar Bauchi ita ta yi na takwas inda ta tara:
N4,567,600.00

Jihar Nasarawa ita ta yi na tara inda ta tara:
N4,477,550.00

Abuja FCT ita ta yi na goma inda ta tara:
N4,078,530.00


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp