Kungiyar Tarayyar Afirka, AU, ta sanar da dakatar da kasar Gabon daga cikin jerin mambobin kungiyar sakamakon juyin mulkin da aka yi a kasar da ke tsakiyar Afirka.
Kwamitin zaman lafiya da samar da tsaro na kungiyar taAU ne ya sanar da hakan a yammacin ranar Alhamis.
Kafin daukar matakin kwamitin ya kuma yi kakkausar suka kan kwace mulki da sojoji suka yi a kasar ta Gabon, juyin mulkin wanda ya yi sanadiyar hambarar da gwamnatin shugaba Ali Bongo.
AU ta ce dakatarwar za ta haramta wa Gabon shiga dukkanin sabgogi da ayyukanta har sai an dawo da tsarin mulkin farar hula a kasar.