Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya ce shugaba Tinubu ya gaza gamsar da cikin yan Najeriya yadda ya samu shaidar kammala karatun jami’a a jihar Chicago ta Amurka.
Atiku a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter a wannan Lahadi ya ce bayanan karatun Tinubu na nuna tamkar bai yi karatun furamare da sakandare ba , jami’a kawai ya yi.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Atikun ke jiran sakamakon da kotun sauraran korafin zabe za ta yanke kan zargin da yake cewa Shugaba Tinubu ya murde masa nasarar da ya samu a zaben da ya gabata.
Category
Labarai