Ana ci gaba da zaman dar-dar yayin da rudani ya mamaye zukatan dalibai da mazauna kewayen jami’ar kimiyya da Fasaha ta jihar Enugu bayan da wasu dalibai har 13 suka mutu sakamakon wata cuta da ba’a santa ba cikin ‘yan makonni.
Wasu daga cikin daliban jami’ar sun
shaidawa jaridar Premium Times cewa abokan karatun su 13 ne suka mutu
cikin kasa da makonni 2 sakamakon wata cuta mai ban tsoro da basu santa ba.
A cewar daliban cikin 13 da suka mutu
guda daya ce kadai aka yi gaggawar kaita asibitin koyarwa na jihar Enugu, inda
ta cika a can, kuma har yanzu ba’a gaya musu dalilin mutuwar ta ba.
Daliban sun kuma kara da cewa da zarar
dalibi ya fara nuna alamun rashin lafiya zai mutu nan take ba tare da bata lokaci
ba, abinda ke kara jefa su cikin razani.
Ko da ta ke karin haske kungiyar dalibai
ta NANS reshen kudu maso gabashin Najeriya ta bukaci mahukuntan makarantar su
yi gaggawar rufe ta don ceto rayukan sauran dalibai.
Ta cikin wata sanarwa da shugaban
kungiyar na shiyyar Kudu maso gabas Chidi Nzekwe ya fitar, ya ce kungiyar ta
damu matuka da irin wannan mutuwa mai ban mamaki, don haka akwai bukatar
mahukunta su yi gaggawar daukar mataki don gano dalili.
Sai dai kuma a wani martanin gaggawa da
shugaban sashen kula da dalibai na jami’ar Jude Udenta ya yi ta cikin sanarwar
da ya fitar, ya yi watsi da bukatar kungiyar dalibai na rufe makarantar.
Ta cikin sanarwar, Mr Udenta
ya musanta labarin cewa dalibai 13 ne suka mutu, yana mai cewa dalibai 5 ne
kachal suka mutu, yayin da yace guda daga cikin su ya mutu ne a sakamakon
hadarin mashin, kuma shi kadai ne ya mutu a cikin makaranta.
“Mu kan mu muna cikin rudani, kuma muna
mamakin irin wannan mutuwa, amma batun mutane 13 sun mutu ba haka bane, tun
farko mu bamu so maganar ta fita bainar jama’a ba, saboda a ganin mu bai dace ana
yamadidi da mutuwar daliban mu ababen kaunar mu a duniya ba” in ji Mr Udenta.
Mr Udenta ya kuma kara da cewa sauran dalibai hudun da
suka mutu sun mutu ne a wajen jami’ar, don haka babu tabbas game da dalilin
mutuwar su, ikirarin da tuni daliban suka musanta, bayan da suka tabbatarwa
manema labarai cewa dukannin dalibai 13 sun mutu a dakunan kwanan dalibai wasu
kuma a cikin aji.
Wannan labari mai cike da sarkakiya dai
tuni ya tilastawa gwamnatin Jihar kafa kwamitin bincike karkashin jagorancin
sakataren gwamnatin Jihar Chidiebere Oniya.
Yayin ziyarar
da kwamitin ya kai jami’ar Mr Oniya ya ce, baya ga binciken, gwamnatin jihar ta
kuma umarci kwamishinan harkokin lafiya Emmanuel Obi da ya gudanar da nasa
binciken daban kan yanayin tsafta, lafiya da ma yanayin da karamin asibitin
shaka ka tafi na jami’ar ke ciki, saboda irin muhimmancin da daliban jami’ar ke
da shi ga jihar.