Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da hukumar kula da da’ar ma’aikata, sun fara binciken shugaban hukumar hana cin hanci da karbar Korafe-korafe na jihar Kano Muhuyi Magaji Rimin Gado kan zargin amfani da karfin gwamnatin tarayya wajen bincken cikin gida.
Muhuyi Magaji Rimin Gado shine jami‘in
da ke tsaye kai da fata wajen tabbatar da zargin cin hanci da Karbar daloli
daga ‚yan kwangila da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Kano Abudllahi Umar Ganduje.
Hukumomin biyu ta cikin wasu mabanbantan
wasiku da suka iakewa hukumar, sun shaida cewa tuni suka fara binciken shugaban ta, kan zargin amfani
da karfin da ya wuce wanda doka ta bashi a kan aikin sa, na binciken tsohon gwamna Ganduje game da bidiyon dala.
Tuni dai wannan sabon bincike ya fara haifar
da ce-ce ku-ce musamman a tsakanin Kanawa wadanda ke ganin Abullahi Ganduje yayi
amfani da sabon mukamin sa na shugaban jam’iyyar APC na kasa wajen shirya wa
muhuyi kulalliya.
Jaridar Premium Times ta ruwato cewa, ko
a lokacin da Gwamna Ganduje ke jagorantar jihar, yayi iya kokarin sa wajen ganin
binciken zargin bidiyon dala da ake yi masa bai yi nasara ba, ta hanyar amfani
da majalisar jihar.
Idan dai za’a iya
tunawa Sabuwar Gwamnatin Abba Gida-Gida ce ta mayar da Muhuyi Magaji Rimin Gado
kan mukamin sa, bayan da gwammnatin Ganduje ta dakatar da shi saboda zargin
wasa da aiki, kuma kememe ta ki mayar da shi duk da umarnin kotu.