Zan samar da tsaron da ko tsakar dare 'yan Nijeriya za su iya fita harkokinsu inji sabon shugaban sojoji

Babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Manjo Janar Taoreeq Lagbaja, ya ce karkashin jagorancinsa, sojoji za su gudanar da aikin samar da tsaron da zai sa al'ummomin dake Neja, Zamfara da sauran jihohin dake fama da matsalolin tsaro za su rika fita harkokinsu ko da karfe biyun dare ne ba tare da sun ji tsoron harin ta'addanci ba.

Janaral Lagbaja ya ce sojoji za su yi aiki sosai a dazukan Birnin Gwari na jihar Kaduna da na Dansadau a jihar Zamfara inda ke da maboyar 'yan ta'adda, ta yadda za su rasa mafaka.

Babban hafsan sojin na magana ne a lokacin da ya karbi bakuncin Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani a hedikwatar tsaro ta kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp