Katsinawa za su san wadanda Dikko zai nada kwamishinoni a makon gobe

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda zai aike da sunayen wadanda zai nada mukamin kwamishinoni a gwamnatinsa ga majalisar dokokin jihar a makon gobe.

Sakataren Gwamnatin Jihar Arch Ahmad Musa Dangiwa ya sanar da hakan a lokacin da ya karbi bakuncin jami'an kungiyar 'yan jarida ta kasa reshen jihar Katsina a ofishinsa.

Sakataren Gwamnatin ya ce tuni Gwamnan ya hada jerin sunayen mutanen da za a nada mukaman, abin da ya rage kawai shi ne a aike da su majalisa don tantancewa da zarar majalisar ta dawo hutu.

Ya ce majalisar ma ta hannun kakaki da mataimakinsa ta tabbatar da shirinta na karbar wadannan sunaye da zarar sun dawo hutu a makon na gobe.

Post a Comment

Previous Post Next Post