An kama jirgin da ya shekara 12 yana satar danyen mai a Nijeriya

A Nijeriya kamfanin NNPCL ya sanar da kama wani jirgin ruwa makare da dayen mai da yawansa ya kai kimanin lita 800,000 da ake zargin na sata ne.

Garba Muhammad, mai magana da yawun hukumar NNPC, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Garba ya bayyana cewa jirgin na dauke da lamba: 6620462, mallakin wani kamfanin Nijeriya ne mai suna HOLAB MARITIME SERVICES LIMITED RC813311.

Haka kuma binciken da aka yi kan ayyukan jirgin da yanzu haka yake a ofishin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta NNPCL ya nuna cewa, jirgin ya shafe shekaru 12 yana gudanar da wannan badakala.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp