An kama barayin da suka saci agwagi da kare a Kano

An kama barayin da suka saci agwagi da kare a Kano

'Yan sintirin Vigilante na garin Gurungawa dake karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun kama matasa hudu da ake zargi da satar wasu agwagi da wani kare.

Kwamandan kungiyar sintirin a garin Abdulhamid Dan'azumi ya ce jami'ansa sun ji motsin matasan da tsakar dare kusan misalin karfe 3 a lokacin da karnuka suka fara haushi a kansu. Bayan jami'an sun isa, suka tarar har sun hallaka kare daya.

Ya ce bayan kama matasan sun amsa laifinsu, kuma an kwace makamai da dama daga wajensu bayan da suka tabbatar da cewa sun dade su na aikata wannan assha.

Daya daga cikinsu, ya sanar cewa sun sa kudi sun sayi karen ne, amma dai agwagin ba na su bane, sun gansu ne suka kwashe suka zuba cikin buhu.

Post a Comment

Previous Post Next Post