Kotu ta hana a tuhumi Hudu Yunusa-Ari


Kotu ta hana a tuhumi Hudu Yunusa-Ari
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta hana hukumar zaben Nijeriya INEC tuhumar kwamishinan zaben da ya ayyana Sanata Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaben Gwamnan jihar Adamawa a zaben 2023.

Mai Shari'a Dotanus Okorowo ya yanke hukuncin hakan, bayan da lauyan Hudu Yunusa-Ari, wato Mr Michael Aondoaka ya bukaci hakan a gaban kotu.

Lauyan Hudu Yunusa-Ari ya shaida wa kotu cewa hukumar zaben INEC ba ta hurumin tuhumarsa har sai kotun sauraren kararrakin zaben ta sanar da makomar dakataccen kwamishina a hukumar zaben.

Post a Comment

Previous Post Next Post