Amai da gudawa bai kama Alhazan Kano ba - NAHCON
Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON ta musanta rade-radin da ake yadawa cewa amai da gudawa ta barke a daya daga cikin masaukan Alhazan jihar Kano dake birnin Makka na Saudi Arabia.
Shugaban tawagar likitocin hukumar NAHCON Dr Usman Galadima ya sanar da hakan a Makka, Saudi Arabia, inda ya ce gurbataccen abinci ne wasu daga cikin Alhazan suka ci daga hannun 'takaru' ya lalata musu ciki.
Ya ce an bude wani cibiyar kula da lafiya ta wucin-gadi a wurin da lamarin ya faru inda ake kula da lafiyar kusan Alhazai 9 da abin ya shafa bayan da suka ci dambu.
Dr Usman ya ce tun daren Asabar, bayan da aka tura tawagar likitoci a wurin, sun shawo kan lamarin, har ma an sallami wadanda suka kamu.
Shugaban tawagar likitocin ya ce duk da shawarwarin da aka ba Alhazan na su guji yame-yamen abinci musamman wanda ba a tabbatar da sahihancinsa ba, amma suka yi kunnen-kashi suka ci.