Wata jarumar fim ta mutu
Jaruma a masana'antar shirya fina-finan Nollywood Sidikat Odukanwi ta mutu bayan fama da rashin lafiya.
'Yar kabilar Yoruba Sidikat ta mutu, bayan fama da rashin lafiyar da ta tilast mata daina fitowa a fim na tsawon lokaci.
Diyar mamaciyar, Bisi Aisha ce ta sanar da mutuwar mahaifiyar tata da aka fi sani da Iyako Oko.
'Yar asalin jihar Osun, an haifi Iyako a shekarar 1960.