Farashin fetur ya kusa linkawa a kasashen Kamaru, Benin da Nijar bayan cire tallafin man a Nijeriya

Farashin fetur ya kusa linkawa a kasashen Kamaru, Benin da Nijar bayan cire tallafin man a Nijeriya

Bayanan da majiyar DCL Hausa ta Daily Trust ta samo sun nuna cewa farashin litar man fetur ya kusa linkawa a kasashen Kamaru, Benin da Jamhuriyar Nijar bayan da Nijeriya ta sanar da cire tallafin man fetur din.

Bayanan sun ce samun fetur din cikin rahusa, ya sa 'yan kasuwa na 'sumogal' dinsa zuwa kasashe makwabta daga Nijeriya har a wuce da shi Sudan wadansu lokutta.

Hakan dai na ba 'yan Nijeriya wahala wajen samun isasshen man da za su yi amfani da shi, da wasu lokuttan akan shiga matsalar karancinsa. Bayanai dai sun tabbatar da cewa cire tallafin man fetur din ya haddasa barazana ga tattalin arzikin kasashen makwabta da yanzu haka harkokin 'bumburutu' suka yi kasa.

Binciken jaridar ya gano cewa ana farashin ya koma CFA700 ko CFA800 a kasar Benin sabanin CFA450 da ake sayarwa kafin a cire tallafin man a Nijeriya.

A baya, ana sayar da litar fetur a Nijeriya kan kudi N195, a kasashe makwabta kuwa ana sayar da litar man kan kudi CFA508 kwantankwacin Naira 381. A haka ne 'yan 'sumogal' ke amfani da damar domin fitar da shi, don a samu kazamar riba.

Post a Comment

Previous Post Next Post