Wasu gungun 'yan daba, sun afka Gidan Rediyon Rock Fm da ke birnin Jalingo na jihar Taraba, in da suka saci kayan aiki masu tarin yawa.
Matasan su sama da dubu biyu, da suka da maza da mata, sun afka shagon wani dan kasuwa, kafin su isa a gidan rediyon. Sai dai bayanan da DCL Hausa ta tattara, sun nuna cewa jami'an tsaro sun yi nasarar hallaka biyu daga cikin wadannan 'yan daba, sannan sun kama da yawa daga cikinsu.
A cikin wata sanarwa daga Ahmad Umar Gassol, daraktan gudanarwa na gidan rediyon, ya ce bata -garin sun afka ofishin nasu ne a a daren Juma'a 21st Yuli, 2023, in da suka suka saci talabijin 2, kwamfitoci, na'urorin nadar sauti, amsa-kuwwa, janareto da kujeru da sauran kayan amfani a gidan rediyo.
Sanarwar ta ce, 'yan dabar sun yi kokarin illata babban jami'in gudanarwar gidan rediyon Mr Oloye Ayodele Samuel, amma ya samu kubuta bayan da jami'an tsaron ciki na DSS da sojoji suka kawo dauki, bayan kiran gaggawa da aka yi musu.
Gidan Rediyon Rock Fm, Jalingo wanda shi ne na farko mai zaman kansa a jihar Taraba, dai na a Unguwar Malam Jada da ke cikin birnin Jalingo a jihar Taraba. Jihar dai na da tarihin ayyukan daba da matasa ke aikatawa. Wasu lokuttan, matasan kan farmaki shagunan al'umma, da ake gudanar da kasuwacin yau da kullum.