Nijeriya ta ji kunya a idon duniya - Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo ya ce shekaru 63 da samun 'yancin kan kasar, har yanzu ba ta yi wani abin a zo a gani ba.

Obasanjo na magana ne a Abuja wajen kaddamar da littafin da tsohon ministan ciniki da masana'antu Olusegun Aganga ya rubuta.

Ya ce a lokacin da kasar ta samu 'yancin kai, ta zamo wata tauraruwa mai haske. Ya ce idan ana son gyara kasar, dole ne sai shugabanni sun amsa laifin cewa akwai matsala.

"Mun ji kunya, mun sa nahiyar Afrika ta ji kunya, mun sa bakaken fata sun ji kunya sannan mun ji kunya a idon duniya". In ji Obasanjo.

Tsohon shugaban kasar ya ce kasar ba ta ajiye kowace kwarya a gurbinta. Ya ce son zuciya ya dabaibaye kowa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp