Wata amarya ta yanke mazakutar angonta a Katsina

Wata mata mai suna Nana da ke da kimanin shekaru 17 ta sa reza ta yanke mazakutar mijinta a daren farko da ya tare bayan ya aure ta a kauyen 'Yar Kyasuwa na karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

Majiyar DCL Hausa a kauyen ta ce mijin mai suna Malam Abubakar ya hadu da matar a lokuttan baya, da yake zuwa zawarci, har ya yi nasarar aurenta. Bayan an daura aure ne, ya tare a daren Lahadi wayewar Litinin, ake zargin ta sa reza ta yanke masa mazakuta.

Har ya zuwa lokacin hada wannan labari, ba a kai ga sanin dalilin wannan mata na yanke wa mijinta wannan hukunci ba. Amma dai, mijin na asibitin Kwandala na garin Malumfashi yana karbar magani.

Sai dai bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce yanzu haka matar ta shiga hannun jami'an tsaron 'yan sanda. Duk da rahotanni sun ce mutumin na jin jiki, bayan wannan aika-aika da ake zargin wannan sabuwar mata ta aikata masa.

Rundunar 'yan sandan jihar ta hannun kakakinta ASP Aliyu Abubakar, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce yanzu haka ana cigaba da gudana da bincike, da zarar an kammala, za a maka matar kotu.

Post a Comment

Previous Post Next Post