Likitoci za su tsunduma yajin aiki a Ingila kan albashi


Kungiyar kananan likitoci a kasar Ingila ta sanar da tafiya yajin aiki na tsawon kwanaki hudu daga karfe 7na safe a ranar 11 ga watan Agusta zuwa 7 na safe a ranar 15 ga watan na Agusta, 2023.

Wannan yajin aiki dai shi ne na baya-bayan nan da likitoci kanana da kwararri da ya yi sanadiyyar dakatar da ganin marasa lafiya.
 
Kungiyar dai na son gwamnatin kasar ta kara wa mambobinta albashi, bayan da ta yi boren cewa abin da ake biyansu ya yi kadan.

Shugaban kungiyar likitocin Dr Robert Laurenson a cikin wata sanarwa, ya ce abin bai yi musu dadi ba, da suka sanar da yajin aikin karo na biyar cikin lokaci kankani.

Yajin aikin da ya gudana a kasar Ingila dai ya haddasa aka jingine ganin marasa lafiya 819,000. 

A farkon wannan watan dai gwamnatin Ingila ta sanar da karin albashi ga ma'aikatan gwamnati, ciki hada likitoci. Inda ta ce kananan likitoci za su samu kaso 6%.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp