Yajin aikin da za ku tsunduma haramtacce ne, sakon FG ga kungiyar NLC

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da kungiyar kwadago ta kasa NLC cewa yajin aikin da take shirin fadawa ya kan halin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa haramtacce ne kamar yadda doka ta sanar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa kungiyar kwadago ta NLC ta ba gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 7 da ta soke aniyarta kan duk tsare-tsaren da suka jefa talakawa cikin mawuyacin hali ko kuma a fuskanci mummunan yajin aiki a kasar.

Sai dai, babbar Sakatariya a ma'aikatar shari'a ta kasar Mrs B.E Jeddy Agba ta sanar cewa kotun kula da ma'aikata ta kasa ta haramta tafiya wannan yajin aiki mai dangane da cire tallafin man fetur.

Ta ce a ranar 5 ga watan jiya na Yuni, kotu ta dakatar da kungiyar kwadago na tafiya yajin aiki.

Sanarwar ta shawarci kungiyar kwadagon da ta bullo da wasu sabbin dabaru ba wai na yajin aiki ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post