Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukaminsa

Shugaban jam'iyyar APC a Nijeriya Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukaminsa na shugabancin jam'iyyar.

Wasu majiyoyi, sun tabbatar wa da jaridar Daily Trust cewa Abdullahi Adamu, wanda tsohon Gwamnan jihar Nasarawa ne ya aike da takardar ajiye mukamin nasa a fadar shugaban kasa, gabanin dawowar Shugaba Tinubu daga kasar Kenya.

Sanata Adamu da ya zamo shugaban jam'iyyar APC na kasa a Maris 2022 bayan zaben shugabannin jam'iyyar, ya aike da takardar ta ofishin shugaban ma'aikata ba fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamilla da yammacin Lahadi.

Wasu majiyoyi sun sanar da majiyar DCL Hausa cewa Sanata Abdullahi Adamu ya gaggauta yin murabus ne bayan da ya jiyo cewa akwai wasu gungun mutane da ke neman yi masa ature.

Post a Comment

Previous Post Next Post