Sojojin Bataliya ta 192 da ke aiki karkashin 81 Div, sun kama wata tirela makare da alburusai da ake kokarin shiga da ita jihar Anambra ta Nijeriya daga kasar Mali.
Mai magana da yawun rundunar soji ta kasa Janaral Onyema Nwachukwu ya sanar cewa an kama wanda ake zargi da safarar wadannan makamai mai suna Mr Eric Seworvor dan asalin kasar Ghana da direban motar.