Ganduje ya fara samun turjiya wajen shugabancin jam'iyyar APC

Tsohon Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fara haduwa da turjiya wajen shugabancin jam'iyyar APC ta kasa kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa mai kula da shiyyar arewa maso yamma Salihu Lukman ya ce maye gurbin Abdullahi Adamu da tsohon Ganduje a shugabancin jam'iyyar kamar kirari ne a daba wa ciki wuka.

Akwai wasu bayanai dai da ke cewa shugaban kasa Bola Tinubu na son Ganduje ya jagoranci jam'iyyar a matakin kasa bayan Abdullahi Adamu ya yi murabus.

A cikin wata sanarwa da Salihu Lukman ya fitar a ranar Alhamis, ta ce ba da sunan Abdullahi Ganduje a matsayin wanda zai rike jam'iyyar har zuwa babban taronta na kasa ba zai haifar wa jam'iyyar da mai ido ba.

Salihu Lukman dai na daga cikin masu fada a ji na jam'iyyar APC a kasa bakidaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post