An samu karin jam'iyyar siyasa a Nijeriya

Hukumar zaben Nijeriya INEC ta sanar da rajistar sabuwar jam'iyyar siyasa mai suna  wato Youth Party (YP).

A cikin sanarwar da kwamishinan hukumar Festus Okoye ya fitar a Abuja, ta ce hukumar ta yi hakan ne karkashin sashen doka na 225 (a) na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Ya zuwa yanzu dai, akwai jam'iyyun siyasa 19 a Nijeriya  bayan soke rajistar jam'iyyu 74 da hukumar ta yi a shekarar 2020 da aka samu da gaza wani katabus a zaben 2019.

A zaben 2019 dai, jam'iyyu 91 ne suka shiga aka dama da su a zaben.

Festus Okoye ya tunaso cewa a watan Agustan 2018 aka yi wa YP rajista domin bin umurnin kotu da ta yi hukunci a 2017.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp