Dan 'sumogal' ya kashe jami’in kwastam a Kebbi

Hukumar Kwastam ta Nijeriya NCS reshen jihar Kebbi, a ranar Lahadin nan ta tabbatar da kisan wani jami’inta mai suna Aminu Abdullahi da ake zargin wani mai safarar motoci ya yi a karamar hukumar Yauri ta jihar.

Kakakin hukumar, ASC Mubarak Mustapha, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi.

Ya ce: “Tuni hukumar kwastam reshen jihar ta Kebbi, ta jajantawa iyalan jami’in Aminu Abdullahi, wanda wani da ake zargin mai safarar mota ne ya kashe a lokacin da yake bakin aiki.

Post a Comment

Previous Post Next Post