Babbar kotun Abuja da ke zama a Maitama, ta ba hukumar tsaron DSS wa'adin mako daya da ko dai ta kai dakataccen Gwamnan babban bankin CBN kotu ko kuma ta sake shi.
Idan zaku iya tunawa dai, Godwin Emefiele ya maka ofishin babban lauyan gwamnati da hukumar DSS bisa kamu da tsare shi da aka yi, inda ya yi zargin cewa hukumomin na yi masa bi-ta-da-kullin siyasa.