Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya umurci da a fitar buhunan hatsi 36,100 domin raba wa masu karamin karfi su samu saukin rayuwa.
Malam Dikko Umaru Radda ya ce ya umurci kananan hukumomi 34 na jihar da su je su sayi masara domin raba wa mabukata su samu sa'ida a rayuwar yau da kullum.
Ya ce an yanke shawarar yin hakan ne domin mutane su samu saukin rayuwa da cire tallafin man fetur ya jawo musu. Ya ma kara da cewa kowa shaida ne ana cikin mawuyacin hali.
Malam Dikko Umaru Radda ya ce gwamnatin tarayya za ta sayar wa gwamnatoci n jihohi da masara, shinkafa da taki, amma a jihar Katsina, za a raba wa talakawa kyauta.