Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya karbi bakuncin jagororin jam'iyyar NNPP na kananan hukumomi da jiga-jigan ta na jiha da suka jingine tafiyar jam'iyyar suka koma jam'iyyar APC.
Shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina Alh Sani Aliyu da sauran kusoshin jam'iyyar APC na jiha ne suka karbi wadanda suka bar NNPP suka koma APC karkashin jagorancin Sanata Abdu Yandoma.
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, a jawabinsa, ya ce jam'iyyar APC na sane da duk irin gudummuwar da suka ba da har aka samu nasara duk kuwa da irin kalubalen da suka fuskanta daga wasu tsirarun cikinsu.
Gwamnan ya kara da cewa 'ya'yan jam'iyyar sun yanke shawarar barin NNPP su koma APC ne bisa radin kansu ba tare da sun gindaya wasu sharudda ba. Ya cigaba yana cewa kawai sun duba cancantar 'yan takarar jam'iyyar APC ne da kuma yadda jam'iyyar ke tsaye kai da fata don ganin jihar Katsina ta cigaba.
A nasa bangaren shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina, Alha Sani Aliyu ya ba da tabbacin cewa daga yanzu sun zama 'yan gida kuma ana bukatar gudunmuwarsu domin kara inganta jam'iyyar APC da ma jihar Katsina bakidaya.
Shugaban jam'iyyar ya ce Mai Girma Gwamna ya nada mashawarta na musamman kan harkokin jam'iyya da siyasa domin samun daidaito da adalci a tsakanin 'ya'yan jam'iyya a jihar.
Tun da farko, tsohon shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Katsina Hon Sani Liti Yankwani da tsohon jigon jam'iyyar ta NNPP Sanata Abdu Yandoma sun yi godiya bisa ga yadda Gwamnan ya karbe su hannu bibbiyu. Sun sha alwashin ba da dukkanin goyon bayan da ake bukata domin tafiyar siyasa ya kara inganta a jihar musamman a zamanin mulkin jam'iyyar APC.