Mulki da mace mataimakiyar gwamma na tayar da kura a Adamawa

Fintiri da Binani

 

A karon farko mutanen jihar Adamawa sun fara sanin muhimmanci ko akasin haka na samun mace mataikiyar gwamna. Nasarar Gwamna Ahamdu Umaru Fintiri wadanda ya dauki mataimakiya Farfesa Kaletapwa Farauta ta biyo bayan rudanin siyasa da ya tilasta gudanar da zaben har sau biyu tare da jinkiri wajen bayyana wanda ya yi nasara a sakamakon zargin wuce gona da iri da kwamishinan zabe na wancan lokacin Hudu Yunusa Ari  ya yi.

Duk da cewa a karshe wannan cece-kuc,  an samu zababben gwamna da kuma mataimakiya, a yanzu wata dambarwa siyasa da ta kunno kai ita ce yadda wasu ‘yan jihar suka zura ido suga yadda za ta kaya a wa’adi na biyu na Gwamna Fintiri sakamakon macen da ya dauka a matsayin mataimakiya. … Na cikin manyan ‘yan’yan jam’iyyar APC a jihar Adamawa da suka yi kokarin ganin Aishatu Ahmad Binani ta yi nasara, ya shaida wa DCL Hausa cewa a yanzu dai za a iya mutanen jihar sun ki cin biri sun ci dila.

Wannan zargi da fargaba da APC ke nunawa kan kamun ludayin mulkin namjij da mace, bai hana jam’iyarr PDP mai mulki a Adamawa ba, ganin alfanun zabin da suka. Jam’iyyar ta PDP ta ce samun wannan hadaka ta jinsi zai ba gwamnatin jihar damar sanin yadda za ta mulki jihar cikin sauki ganin yadda yanzu mace take a matsayin mataimakiyar gwamna.

Duk dai wannan musayar yawu da ‘yan siyasa ke  yi suna yi ne don al’ummar jihar, sai dai kuma mutane sun kasa kunne tare da zuba idon ganin yadda za ta kaya a wannan mulki “samfurin shinkafa da wake” karon farko a tarihin jihar.

Kungiyoyin mata na ganin shigar da mata a harkar shugabanci abu ne da zai kawo wa jihar Adamawa ci gaba ta bangarori dabam-dabam. Asma'u Suleiman Surko dake Rajin kare hakkin mata ta  Shaidawa DLC HAUSA cewa samun mace a wannan muƙamin babban Nasara ce ga al'umma.

Kawo yanzu dai jama’a a jihar Adamawa cike suke da zumudin ganin sauyin da gwamnatin Gwamna Ahmadu Fintiri za ta nuna wa jihar da ya banbanta da wa’adinsa na farko wanda ya yi mulki da namiji a matsayin mataimaki.

 

DLC HAUSA,  A'isha Usman Gebi daga Yola

Post a Comment

Previous Post Next Post