Mutanen Kaduna na fargabar rusau daga Uba Sani

Ayyuka na farko-farko da Uba Sani ya fara yi a matsayin sabon gwamnan jihar Kaduna a ranar 29 ga watan Mayu, sa’o’I kadan bayan da aka rantsar da shi, su ne sanar da sauya sunan sanannen titin nan na Rabbah Road zuwa Malam Nasir El-Rufa’i road, abin da ya razana wasu da suka yi fatan sabon gwamnan ya kauce wa manufofin tsohon gwamnan da aka yi wa lakabi da “mai rusau”. An zargi El-Rufai dai da bijirowa mutanen jihar da manufofi masu tsauri a zamanin mulkinsa. To sai dai kuma wasu na ganin hakan ba wani abu ba ne illa godiya da girmamawa ga tsohon gwamnan, ganin irin tsayin dakar da Elrfufai ya yi wajen ganin Uba Sanin ya zama gwamna.


Cikin manyan alkawurran da gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi wa jama’ar akwai tabbatar da tsaro, alkinta tattalin arziki da janyo masu zuba jari sai kuma hada kai tare da tafiya da kowa ba tare da nuna banbancin bangaranci addini, kabila ko kuma siyasa ba.


Batun siyasa na ci gaba da dumama a jihar ta Kaduna, musamman la’akari da yadda kotun sauraren kararrakin zabe ta fara zaman sauraren karar da jam’iyyar PDP ta shigar, tana Kalubalantar sakamakon zaben, wanda ta ce an yi aringizo, da kuma amfani da kudade wajen wannan zabe, baya ga tafka magudi.

Da bambancin kuri’u kasa da dubu 12 ne dai APC ta lashe zaben gwamna, abin da watakila ke ba PDP kwarin gwiwar samun nasara a kotu. 

To ko me ‚yan adawa a jihar zasu ce a game da wannan zaman shari’a da aka fara da kuma kamun ludayin gwamnatin da Uba Sani a Kaduna, Muhammad Dan Auta mai bai wa shugaban jam’iyyar PDP a jihar a Kaduna shawara ta fannin yada labarai, ya ce da alamu gwamnatin bata shigo da kafar dama ba, kasancewar ta shiga a cewarsa ta hanya mai cike da kazanta.

Da alama wadannan kalamai basu yiwa gwamnatin da magoya bayanta wani tasiri ba, don kuwa a cewar su basu da ko dar cewa sune zasu yi nasara a kotun,Muhammad Sani Akilu Idris shi ne mataimakin tsohon gwamna El-Rufa’I kan harkokin siyasa, yace akwai alamun haske idan aka lura da kamun ludayin gwamnan jihar cikin mako guda.

A yayin da jam’iyyu APC da PDP ke ci gaba da tabka zazzafar siyasa bisa kamun ludayin gwamnatin APC, mutanen jihar sun shaida wa DCL Hausa abubuwan da suka fata da kuma zullumi daga gwamnatin gwamna Uba Sani

Jihar Kaduna da ake yiwa kallo da cibiyar arewacin Nijeriya na da matukar tasiri wannan ta sa siyasarta ke daukar hankali, duk da dai jama’ar jihar na ganin akwai jan aiki gaban sabon shugaba Uba Sani.

 


DCL Hausa, Yacouba Umaru Maigizawa

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp