Muna goyon bayan Tinubu da ya cire tallafin man fetur - CNG


 Muna goyon bayan Tinubu da ya cire tallafin man fetur inji kungiyar da ke kishin arewa 


Kungiyar nan da ke rajin ganin yankin arewacin Nijeriya ya cigaba da ake kira da CNG a takaice ta fito karara ta nuna goyon bayanta ga matakin shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur.


Kungiyar mai hadakar kungiyoyi 150 ta caccaki tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, inda ta ce kudin da ake kashewa na tallafin man fetur Dala bilyan 15.6 a duk shekara ya isa a gina layin dogo daga Lagos zuwa Kano da kuma daga Port Harcourt zuwa Maiduguri da kuma Lagos zuwa Calabar.


Mai magana da yawun kungiyar Abdul'aziz Sulaiman a cikin takardar bayan taro da ya karanta a Kaduna, ya ce Naira tiriliyan 2.91 da gwamnatin Buhari ta kashe kan tallafin man fetur daga Janairu zuwa Disambar 2022, ne ya sa tattalin arzikin kasar ya durkushe.

Post a Comment

Previous Post Next Post