Cinikin fetur ya ragu matuka a mafiyawancin gidajen man Nijeriya bayan cire tallafin man
Tashin gwauron zabin da farashin man fetur ya yi sanadiyyar cire tallafin man, ya sa gidajen mai babu ciniki sosai a 'yan kwanakin nan a Nijeriya.
Wani bincike da Daily Trust ta gudanar, ya nuna cewa bayan farashin fetur din ya koma N537 a mafiyawan gidajen man, mutane sun fara kaurace wa, babu ciniki sosai.
Mafiyawan gidajen man, akwai man amma babu masu saye, har ma an gano cewa wasu mutane sun ajiye motocinsu ta dalilin tsadar fetur din.
Wani Manajan gidan mai a Kano, ya shaida cewa a baya, cikin kwanaki biyu suke sayar da fetur din su, amma yanzu yana iya cike mako cur ba a sayar ba.