Ta leko ta koma shi ne abin da wasu ma’aikata suka shaida sakamakon sauyin gwamnati da aka samu jihar Sokoto. A cikin kasa da sa’o’I 24 da tsohon gwamna Tambuwal na jam’iyyar PDP ya mika mulki ne dai, sabuwar gwamnatin jihar ƙarƙashin jãgorancin gwamna Ahmad Sule na jam’iyyar APC ta ɗauki matakin sõke daukar ma'aikata da ƙãrin girma da gwamnatin Aminu Waziri Tambawal ta yi, lamarin da ya sanya da dãma daga cikin waɗanda aka ɗauka aikin cikin halin ni ƴãsu. Daya daga cikin mutanen da tsohon gwamna Tambuwal ya dauka aiki a jihar ya shaida wa DCL Hausa yadda suka ji da kamun ludayin sabuwar gwamnmatinwacce ya zarga da jefa rayuwarsa cikin kunci.
Ita dai sabuwar gwamnatin ta ce irin wadannan ayyuka da tsohon gwamnan PDP Tambuwal ya rarraba wa mutanen da ta kira “shafaffu da mai” abu ne da aka yi cikin kuskure wanda ba za ta lamunta ba, a don haka ne ta ce duk wani karin girma ko daukar aiki da Tambuwal ya yi bayan zaben gwamnan jihar daga ranar 19 ga watan Maris zuwa na ranar da aka mika mata mulki to ta warware shi. Sai dai kakakin PDP a jihar ta Sakkwato Hassan Sahabi Sanyinnawal yace abin da sabuwar gwamnatin jihar ta yi bīta da ƙulli na siyasa ne kawai.
Duk ƙoƙarin da nayi, har tsawon kwanaki biyu, dan jin ta bakin ɓangaren sabuwar gwamnatin ta jihar Sakkwato, dan jin dalilin soke daukar aiki da kuma ƙarin girma ga wasu ma'aikata yaci tura.
Wani mai sharhi kan lamurran siyasa, Dakta Umar Adamu na jami'ar jihar Gombe yace, irin wannan mataki kan iya haddasa gãba a tsakaninin alumma.
Da alama dai irin wannan fashin baki da tirjiyar da sabbin am’aikatan da aka dauka ke nunawa ba za su sanya sabuwar gwamnatin ta jam’iyyar APC dawo da ma’aiaktan na Sokoto bakin aiki ba, inda baya ga korar wadannan malamai, sabon gwamna Ahmed Sule ya umurci a soke sababbin sunayen da tsohon gwamna Tambuwal ya rada wa wasu manyan makarantun jihar.
DCL Hausa, Umar Ibrahim